Ilimi

Yadda Gwamnan Nasarawa Ya Jagoranci Buɗe Sabon Ofishin WAEC Na Zamani

Gwamnan jihar Nasarawa, Engr. Abdullahi A. Sule, ya jagoranci buɗe sabon ofishin hukumar shirya jarrabawar kammala Makarantun Sakandire ta yammacin Afirka (WAEC) na zamani, a Lafia babban birnin jihar, a jiya (Talata).

A ya yin ƙaddamar da Ofishin, Gwamnan ya buƙaci Gwamnati, da ma ƙungiyoyi masu zaman kansu da su bada dukkannin gudunmawarsu wajen tabbatar da haɓɓa fannin Ilimin ƙasar nan.

Gwamnan ya kuma ce, haƙiƙa Gwamnatinsa na yin dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da bunƙasuwar Ilimin yaran jihar, inda ya buƙaci agajin hukumomin Gwamnatin tarayya, da ma ƙasashen ƙetare wajen tallafawa bunƙasuwar Ilimi a ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma ce, Gwamnatinsa na ƙarfafar dukkannin hukumomin gwannatin da su ke aikin bunƙasa Ilimi a kowanne mataki, ya na mai alƙawarta tallafawa Ofishin hukumar ta WAEC da ke Lafiya, da Motocin Zirga-Zirga.

A nasa jawabin, Kwantirolan hukumar WAEC na ƙasa, Dr. Amos Dangut, godewa gwamnatin jihar ya yi, bisa gwangwaje su da ta yi da kantamemen filin gina ofishin, a ya yin da hukumar ke ta ƙoƙari wajen sauya tsarin jarrabawarta, daga takarda da fensiri, zuwa Na’ura maiƙwaƙwalwa, domin dacewa da cigaban zamani.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button