Zamantakewa

Yadda Yunƙurin Sanata Hanga Na Gwangwaje Maƙabartun Kano Da Tukwane, Ke Cigaba Da Tada Ƙura

Sanatan shiyyar Kano ta tsakiya, Rufa’i Hanga, ya ce zai rabawa ƙananan hukumomin Kano ta tsakiya, tukwane 3,000 tare da likkafani.

Mai Magana da yawun Sanatan, Abdulhamid Namadobi, ya ce Sanatan ya ƙudiri aniyar yin hakan ne, sakamakon koke-koken da ya samu, na rashin Tukwanen, a maƙabartun Kano ta tsakiya.

Bugu da ƙari ya ce, Sanatan zai raba Likkafani yadi 10,500 domin siturta mamata, kamar yadda addini ya tanada.

Sai dai, wannan mataki na cigaba da yamutsa hazo a kafafen sada zumunta na zamani, inda al’umma da dama ke fassara hakan a matsayin fito da manufar shuwagabanni ƙarara ta hallaka ƴan Najeriya, sakamakon irin halin ƙuncin da ake cigaba da fuskanta.

A gefe guda kuwa, wasu mutanen na kallon hakan a matsayin gagarumin cigaba, duba da yanayin da ake fuskanta na ƙarancin tukwanen a maƙabartu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button