Yadda Za Ku Gyara Kwanan Watan Haihuwarku Na Katin Ɗan Ƙasa, A Wayar Hannu
Ba kamar yadda aka saba a baya ba, a yanzu gyaran bayanan katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN Slip) ya ƙara sauƙi, sakamakon ɗumbin matakan da hukumar NIMC ke ɗauka.
GA YADDA ZA KU GYARA KWANAN WATAN HAIHUWARKU NA NIN DA HANNAYENKU :
• Ku halarci adireshin: selfservicemodification.nimc.gov.ng/, ku yi rijista, ku yi login, sannan ku yi verification na NIN ɗinku, da hoton fuskarku.
• Sai ku danna maɓullin, ‘Date Of Birth Modification’, Sannan ku biya kuɗin gyaran da za ku yi.
• Sannan ku saka lambar Katin Haihuwarku na zamani (Digital NPC Birth or Attestation Certificate Number). Za ku iya samun NPC Certificate ta hanyar halartar adireshin: https:attestation.nationalpopulation.gov.ng/.
• Daga nan sai ku yi uploading na NPC Certificate ɗinku, tare da sauran dukkannin bayanai, da takardun da ake buƙata, ku yi ‘Submit’ (Ku tabbatar kun yi checking ɗin akwatin attestation, domin kammala miƙa bayananku).
• Shikenan kun kammala, za kuma a sanar da ku, da zarar gyaranku ya yi approved. Sannan za a aike muku da sabon Slip ɗinku ta Email (za kuma ku iya downloading ɗinsa ta dashboard ɗinku).
Rubutawa : Miftahu Ahmad Panda.
08039411956