Yadda Za Ku Kalli Hukuncin Zaɓen Gwamnan Kano Kaitsaye, Daga Ko Ina Kuke
Ƙarancin Jama’ar da Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar Kano, ta amince su shiga cikin harabar Kotun domin kallon yadda ake zartar da hukunci kaitsaye, ya sanya al’umma da magoya bayan jam’iyyu da dama sun rasa damar ganin yadda hukuncin ke kasancewa.
Mutum 50 kacal, Kotun sauraron ƙarar zaɓen ta amince su shiga cikin farfajiya domin kallon hukuncin, wanda ake tsaka da zartarwa yanzu haka, ta Allon Gani-Gaka.
Jaridar Rariya Online, zaƙulo muku yadda za ku shiga wurin da ake zartar da hukuncin kaitsaye ta Manhajar Zoom, domin kallon yadda ta ke wakana.
Ga Matakan da za ku bi:
•Ku buɗe Browsers ɗin wayoyinku, ko Computer, Sannan ku saka adireshin: https://us04web.zoom.us/j/3678773793, sai ku yi Join.
Ko kuma ku sauke Manhajar Zoom, daga rumbun Adana Manhajoji na Playstore, ko Appstore, Sannan ku shiga ciki ku yi rijista.
Sai kuma ku shiga wurin Join Meeting, ku sanya: 367 877 3793 a matsayin Meeting ID, sai kuma PWU46d a matsayin Password.