Yajin Aikin Ƙungiyar Likitoci Haramtacce ne – A cewar Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta bayyana yajin Aikin gargadin da kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ke yunkurin farawa na kwanaki biyar, a yau, a matsayin haramtacce. Ta na mai cewar, Kungiyar bata bawa Gwamnati wa’adin kwanaki 21 na gargadi ba, kamar yadda ya ke a kundin dokokin kwadago.
Mai magana da yawun maáikatar kwadago da nagartar Aiki, Olajide Oshundun, shi ne ya bayyana hakan a ya yin zantawarsa da jaridar Daily Trust, inda ya ce Minista ya karbi wasikar kungiyar ta NARD ne, a ranar Talata. Ya na mai cewar, wasikar na dauke ne da kwanan watan 15 ga watan Mayun 2023, wanda kuma kamata ya yi a ce kungiyar ta bada waádin kwanaki 21.
Idan mai sauraro bai manta ba dai, ko a ranar 29 ga watan Afrilun da ya gabata sai da kungiyar ta tsunduma Yajin Aikin gargadi na makonni biyu, da nufin tilasta gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da ke tsakaninsu. Inda kuma waádin ya kare a ranar Asabar.
Bukatun kungiyar dai, sun hadar da sauya fasalin albashin maáikatan lafiya da kaso 200 na albashin da su ke karba a yanzu; da ma kara musu kudaden alawus-alawus kamar yadda su ka zayyana a wata wasika da kungiyar ta aikewa minista a ranar 7 ga watan Yulin 2022; sai kuma biyan kudin horon likitocin masu neman kwarewa; da biyan kudaden ariya na albashi, da ma kara mafi karancin albashi. Da sauran bukatu.