Yajin Aikin Ƙungiyoyin Ƙwadago Ya Tilasta Dakatar Da Jarrabawar Qualifying, A Kano
Wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta fitar, ta bayyana dakatar da rubuta jarrabawar neman cancantar samun tallafin rijistar jarrabawar NECO, da Ɗaliban Aji Biyar na makarantun Sakandiren jihar ke rubutawa (QUALIFYING), daga ranar Talata, 14 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, har sai abinda hali ya yi.
Bayanin dakatarwar, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa, da Daraktan Wayar Da Kan Jama’a na Ma’aikatar, Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanyawa hannu, inda sanarwar ta bayyana cewar, an dakatar da rubuta jarrabawar ne, biyo bayan matakin da gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC su ka ɗauka, na tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, a faɗin ƙasar nan.
Sai dai sanarwar, ta buƙaci Iyaye da Ɗalibai da su kwantar da hankulansu, domin kuwa dakatar da jarrabawar da aka yi, bashi da wata matsala ko illa da zai haifar.