YAN SANDA SUN TSARE MA’AIKACIN LIBERTY SABODA WASU ALMAJIRAI
Wadannan da kuke gani sune almajiran da suka sa yan sanda suka tsare ma’aikacin gidan talabijin da radiyo na liberty dake Abuja, Tundai da farko Masa’ud da Ibrahim an kawo su karatun allo ne daga karamar hukumar sumaila ta jihar Kano zuwa keffin jihar Nassarawa amma Sabo da basa son karatun allon da kuma duka da sukace malaminsu Yana musu shine suka gudu.
Wadannan yara sun taka daga keffin har zuwa unguwar Mpape karamar hukumar mulki ta Bwari Dake Abuja, daga nan aka kawosu offishin liberty kasancewa ishaq sa’eed Hamza ma’aikacin tashar ne kuma a keffi yake da zama tare da iyalansa, shine daga ofis aka yanke shawarar ya Taho dasu Dan yaga Malamin in yaso a mayar dasu gaban iyayensu maimakon a barsu su shiga duniya ba’asan hannun da zasu fad aba.
Ishaq sa’eed Hamza yana isa A Y A da nufin shiga Motar da zata kaisu keffi sai kawai Wani Dan Sanda yace yafito daga motar yana zare masa ido yana cewa ai sato yaran yayi. Nan take ya ciro katin shaidar aikin jarida wato ID Card ya nuna Dan Sanda yace sam baisan wannan maganar ba ai kawai shi barawon yarane nandai ishaq yayi jawabi na fahimta da zaisa a gamsu Amma ina Dansanda Abokin kowa yayi ke meme.
Daga bisani dai bayan anyi sabatta juyatta an yamutsa gashin baki tare dayin manyan turanci da kanana daga karshe dai an hadashi da daya daga cikin Jami’an ‘yan Sanda daga A Y A zuwa keffi Domin Tabbatar da Gaskiya.
Bayan sun iso garin Keffi ya nemi shugaban Alarammomin keffin wanda dama tuni tun daga office an sanar da shi cewa yaran na hannun hukumar tashar yanci liberty tv da radio kuma sun gana da shugaban kungiyar Alarammomin da kuma Malamin yaran wanda yanzu haka dai ankira mahaifin yaran ya kuma tabbatar da cewa zai turo kudin mota a mayar dasu gida suyi karatu a kusa da shi.
Daga karshe Ishaq sa’eed Hamza ya yi kira ga iyaye inda yake cewa Dan Allah iyayen Yara akula da Amanar da Allah ya bayar, Yara masu Karanci Shekaru arika hakuri suyi karatu a gida maimakon tura su nesa Neman karatu.
Wannan shine ake kira dakyar nasha yafi da kyar aka kamani.