Yanzu Masu Garkuwa Da Mutane Sun Karye, Saboda Ƙarancin Kuɗi – A cewar Ngige
Ministan ƙwadago da nagartar Aiki, Chris Ngige, ya bayyana cewar, tsarin taƙaita amfani da takardun kuɗi, da babban bankin ƙasa (CBN) ya ɓullo da shi, abu ne da ya ke da tarin alfanu, duk kuwa da ƙalubalen da ya ke ɗauke da su.
Ministan, wanda ya bayyana hakan, ranar Laraba, ta cikin shirin Politics Today, na gidan Talabijin ta Channels, ya musanta batun da wasu ƴan Najeriya ke yi, na cewar, alfanun tsarin bai taka kara ya karya ba.
Ngige ya ce, tsarin na yi wa al’ummar Najeriya ciwo ne, sakamakon tasgaron da aka fuskanta wajen aiwatar da shi.
Ya na mai cewar : ”Tsarin kam ba a aiwatar da shi yadda ya kamata ba. Na yarda da haka. To amma tsarin mai kyau ne ?, Eh, ya na da kyau.
”Za mu ga cewar, mutane basu sayi ƙuri’a ba, a layukan zaɓuka.
”Na je zaɓe, kuma na ga hakan. Kuma kaga su ma masu garkuwa da mutane sun karye, sun shiga yajin aiki, ko mu ce masassarar tattalin arziƙi. Haka abin ya ke ga ƴan bindiga, su ma suna cikin hutu”.