Labarai

Yanzu-Yanzu: Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Tsunduma Yajin Aiki

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun tsunduma Yajin Aiki a yau (Talata), 14 ga watan Nuwamban 2023.

Bayanin umarnin tsunduma Yajin Aikin ƙungiyoyin, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da Manyan Sakatarorin ƙungiyoyin biyu, na NLC, Comrade Emmanuel Ugboaja; da na TUC, Comrade Nuhu Toro, su ka sanya wa hannu, tare da fitar da ita, da yammacin ranar Litinin ɗin da ta gabata, 13 ga watan Nuwamba.

Sanarwar dai, ta buƙaci ɗaukacin membobin ƙungiyoyin guda biyu, da su ƙauracewa wuraren ayyukansu, daga ƙarfe 12:00 na daren yau.

NLC da TUC dai, sun ɗauki matakin tsunduma Yajin Aikin ne, bayan da su ka zargi Gwamnatin tarayya da gaza cika musu alƙawurran da ta ɗauka, kafin amincewa su jingine yajin aikin da su ka shirya tsunduma tun a baya.

Idan ba a manta ba kuma, a ƙarshen makon da ya gabata ne, Kotun ɗa’ar Ma’aikata ta umarci ƙungiyoyin na NLC da TUC da su ƙauracewa tsunduma Yajin Aikin, bayan wata buƙatar gaggawa da Gwamnatin tarayya ta shigar gaban Kotun kan lamarin, inda a gefe guda ƴan ƙwadagon su ka bayyana cewa, har yanzu ba su karɓi umarnin hakan daga Kotun ba.

A gefe guda kuma, wasu na zargin ƙungiyoyin sun tsunduma Yajin Aikin ne, da nufin bayyana fushinsu, kan dukan kawo wuƙa da Jami’an Ƴan Sanda, su ka yi wa shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero a jihar Imo, makonni biyu da su ka gabata, ya yin da ya halarci jihar, domin jagorantar gudanar da zanga-zanga.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button