Yanzu-Yanzu: An Samu Tangarɗar Igiyar Sadarwa (Network) Ya Yin Da Ake Tsaka Da Zartar Da Hukunci Kan Zaɓen Gwamnan Kano
An samu katsewar igiyar Sadarwa, a ya yin da Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar Kano, ta ke tsaka da karanta hukunce-hukunce kan ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar a gabanta ta na ƙalubalantar nasarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, a zaɓen da aka gudanar cikin watannin farkon shekarar nan.
Katsewar network ɗin kuma, ta zo ne bakatatan a ya yin da ake tsaka da sauraron hukuncin, inda a yanzu Lauyoyi, Wakilan jam’iyyu, da ma Ƴan Jaridu ke cigaba da dakon dawowar igiyar Sadarwar domin cigaba da karanta hukuncin.
Wakilan da su ka rabauta da shiga harabar Kotun daga tsagin jam’iyyar NNPP mai mulki, su ne:
1. Dr. Baffa Bichi.
2. Hon. Shehu Wada Sagagi.
3. Prof. Hafiz Abubakar.
4. Engr. Marwan Ahmad.
5. Dr. Hashimu Dungurawa.
6. Dr. Hamisu Sadi Ali.
7. Baba Halilu Dantiye.
8. Sanusi Bature Dawakin Tofa.
9. Hon. Ladidi Garko.
10. Hajiya Aisha Saji.
11. Hon. Jamilu Lawan Saji.
13. Engr. Muhammad Diggol.
14. Air Commodore Yusha’u Salisu.
Sai kuma wakilan APC, da su ka haɗar da:
1. Hon. Ibrahim Zakari Sarina.
2. Hon Badara Ungoggo.
Zuwa yanzu dai, Kotun ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe guda biyu, daga cikin guda uku, da Jam’iyyar APC ta gabatar a gaban kotun.