Yanzu-Yanzu: An Sanar Da Sakamakon Zaɓen Ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni Ta Kano
Kwamitin shiryawa, tare da gudanar da zaɓen ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta ƙasa, reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin, Abubakar Shehu Kwaru, na tashar Talabijin ta Sa’adatu Rimi, ya sanar da sakamakon zaɓen sababbin shuwagabannin ƙungiyar, bayan ƙuri’un da membobinta su ka kaɗa.
Da safiyar yau (Alhamis) ne dai, membobin ƙungiyar su ka gudanar da zaɓen sababbin shuwagabanni, a Ma’aikatar wasanni ta jihar Kano.
Zaɓen ya samu halartar Babban Sakataren Ƙungiyar ta SWAN na ƙasa, Ikenna Okonko, da tsohon mataimakin shugabanta na shiyyar Arewa Maso Yamma, Lurwanu Idris Malikawa.
Sauran mahalarta filin gudanar da zaɓen su ne: Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, shugaban Alƙalan wasanni na jiha, Manema Labarai, da sauran jama’ar gari.
Ga Jerin Sunayen Sababbin Shuwagabannin:
•Zaharadeen Sale, daga Pyramid Radio a matsayin Shugaba.
•Abubakar Muhammad Jibrin, daga Guarantee Radio, a matsayin Mataimakin shugaba.
•Auwal Salisu, daga tashar Talabijin ta NTA Kano, a matsayin Sakataren Kuɗi.
•Mubarak Muhammad Sani, daga BUK FM, a matsayin Jami’in Walwala.
Dukkannin waɗannan sababbin shuwagabanni dai, za su shafe tsawon shekaru uku ne, a zangon shugabancinsu.