Yanzu-Yanzu: Daurawa Ya Koma Kujerar Shugabancin HISBAH
Wasu rahotanni da ke fitowa yanzu-yanzu daga fadar gwamnatin Kano, sun bayyana yadda aka samu sulhu tsakanin shugaban hukumar HISBAH, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a daren Litinin ɗin da mu ke ciki, inda a yanzu Malamin ya amince da komawa kujerarsa ta shugabancin HISBAH.
Wannan cigaba na zuwa ne, jim kaɗan bayan kammala tattaunawar Majalissar Malaman Kano, tare da Sheikh Daurawan, da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Tattaunawar ta sa’a guda, ta kuma taɓo sauran muhimman fannoni da ke da alaƙa da rayuwar al’umma, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana.
Idan za a iya tunawa dai, a ƙarshen makon da ya gabata ne, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana yin murabus ɗinsa daga shugabancin hukumar HISBAH ta Kano, ta cikin wani gajeren bidiyo mai mintuna biyu, da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta ta Facebook.
Matakin da Malamin ya ɗauka kuma, ya zo ne sakamakon wasu kalamai da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya furta akan ayyukan hukumar, waɗanda Malamin ya ce sun karya masa guiwa ƙwarai da gaske.
Sai dai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce, daman Malamin bai aikewa Gwamnati wasiƙar ajiye Aikinsa a rubuce ba, saboda haka bayan samun wannan sulhu, Malamin zai koma ofis domin cigaba da gudanar da ayyukansa a safiyar gobe (Talata), 5 ga watan Maris ɗin da mu ke ciki.