Kotu

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Ya Sauke Kwamishina, Bisa Barazanar Hallaka Alƙalai

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Kwamishinan ma’aikatar ƙasa da safayo na jihar, Adamu Aliyu Kibiya, tare da Mai bashi shawara kan al’amuran Matasa da wasanni, Ambasada Yusuf Imam (Ogan Ɓoye), bisa zarginsu da furta wasu kalamai na barazana ga Alƙalan Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar, a ranar Alhamis, wanda hakan ke nuna rashin mutuntawa ga fannin Shari’a.

Bayanin hakan kuma, ya fito ne, a ya yin taron manema labarai, da Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Baba Halilu Dantiye ya kira, inda ya ce Gwamnatin Kano ba ta da alaƙa da kalaman da mutanen biyu su ka furta, domin kuwa sun furta kalaman ne bisa raɗin kansu.

Ka zalika, ya bayyana cewar, Gwamnatin Kanon na sake yin kira, tare da jan hankalin Jami’anta da su gujewa furta kalaman da basu da alaƙa da ofisoshin da aka kallafa musu Alhakin lura da su.

Kafin ɗaukar wannan mataki dai, daman ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa (NBA) ta buƙaci Gwamnan na Kano, da ya tsige Kwamishinan bisa furta kalaman da su ka ƙunshi barazana ga Alƙalai.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button