Labarai

Yanzu-Yanzu: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Nasarar A.A. Sule, Bayan Watsi Hukuncin Kotun Farko

Kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta yi mi’ara koma baya kan hukucin da Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Nasarawa ta yanke, wanda ya baiwa ɗan takarar jam’iyyar PDP, David Ombugadu nasara, tare da sutale Gwamna Abdullahi Sule na APC daga kan kujerar jagorancin jihar ta Nasarawa.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ce dai, ta ayyana Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan jihar, da aka gudanar, a watan Maris ɗin shekarar da mu ke ciki, inda rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen ya sanya ɗan takarar PDP, David Ombugadu garzayawa gaban Kotun sauraron shari’ar zaɓe, ya na ƙalubalantar nasarar ta A.A. Sule.

A wancan lokacin kuma, INEC ta ce, A.A. Sule ya lashe zaɓen Gwamnan jihar ne, da kimanin ƙuri’u 347,209, inda ya doke abokin karawarsa na PDP da ke da jimillar ƙuri’u 283,016 a zaɓen.

Sai dai, a cikin hukuncin da ta yanke, tun a ranar 2 ga watan Oktoban da ya gabata, Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar, ta soke nasarar ta Gwamna A.A. Sule, tare da ayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Hakan kuma ya sanya Gwamna A.A. Sule, ta hannun Lauyansa, Wole Olanipekun (Mai lambar anini ta SAN) garzayawa gaban Kotun ta ɗaukaka ƙara, tare da roƙonta da ta yi watsi da hukuncin Kotun sauraron shari’ar zaɓen.

Olanipekun, ya kafa hujja da cewar, Kotun sauraron shari’ar zaɓen bata basu damar gabatar da shaidu ba a ya yin da ake sauraron shari’ar, ya na mai ƙarawa da cewar, Kotun ta kuma yi watsi da bayanan da na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’u ta BVAS ta naɗa, inda taƙi karɓarsa a matsayin hujja.

Da safiyar yau (Alhamis) ne kuma, Kotun ɗaukaka ƙarar mai Alƙalai Uku, ta bayyana cewar, hukuncin Kotun sauraron shari’ar zaɓen ya ci karo da doka, ta na mai wuƙar ƙugu da cewar, A.A. Sule ne ya lashe mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa a ya yin zaɓen.

Kotun kuma ta jingine hukuncin, tare da sake ayyana Gwamna Abdullahi Sule, a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar Gwamnan jihar ta Nasarawa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button