Siyasa

Yanzu-Yanzu: Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe Ta Sake Tabbatar Da Nasarar Sagir Ƙoki

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan Majalissu da ke zamanta a Kano, ta kori ƙarar da tsohon ɗan majalissar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano (Kano Municipal), Muntari Ishak, na Jam’iyyar APC, ya shigar gabanta, ya na ƙalubalantar nasarar da sabon zaɓaɓɓen Ɗan Majalissar yankin, Engr. Sagir Ƙoki, na jam’iyyar NNPP ya samu.

Kotun ta kuma buƙaci tsohon ɗan majalissar, da ya biya tarar Naira Dubu Ɗari Uku (300,000), sakamakon ɓatawa waɗanda ya ke ƙara lokaci da ya yi.

Kotun dai, ta ce ta kori wannan ƙara ne, sakamakon gaza gabatar mata da gamsassun hujjoji, daga ɓangaren masu ƙara.

Ko a ɗazu ma dai, sai da Kotun sauraron ƙararrakin zaɓuɓɓukan ƴan Majalissar wakilan, ta sake tabbatar da nasarar Ɗan Majalissa Mai wakiltar ƙananan hukumomin Wudil da Garko, Abdulhakim Kamilu Ado, na Jam’iyyar NNPP, bayan da ta yi watsi da ƙarar da tsohon ɗan majalissar yankin, Muhammad Ali Wudil ya shigar gabanta, ya na ƙalubalantar nasarar sabon ɗan majalissar.

Kotun kuma, taci tarar, Ali Wudil ɗin Naira 800,000 sakamakon ɓata lokacin waɗanda ya ke ƙara.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button