Addini
Yanzu-Yanzu: Sarkin Musulmi Ya Sanar Da Ganin Watan Ramadan, A Najeriya
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Azumin Ramadan, a Najeriya.
Sarkin, ya sanar da ganin watan ne, a daren Lahadi, 29 ga watan Sha’aban, wanda ya yi dai-dai da 10 ga watan Maris ɗin 2024.
Hakan kuma na nufin, gobe (Litinin) za ta kasance 1 ga watan Ramadana, bayan al’ummar Musulmi sun tashi da Azumi.
Kafin sanar da ganin watan a Najeriya dai, ƙasashe da dama ciki har da Saudiyya, sun sanar da ganin watannin a ƙasashensu.
A madadin ɗaukacin shuwagabanni da ma’aikatan Jaridar Rariya Online, muna yi muku barka da shigowa watan Ramadan.