Kasuwanci

Yanzu-Yanzu: Shafukan Facebook Da Instagram Sun Dawo Aiki

An samu ɗaukewar shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram, a yammacin ranar Talata, a faɗin duniya.

Shafukan guda biyu, waɗanda mallakin kamfanin Meta ne, sun ɗauke, tare da bada matsaloli iri daban-daban ga masu amfani da kafafen, kama daga fitar da mutane daga asusansu, hana refreshing na news feed, rashin buɗewar manhajojin shafukanma baki ɗaya, da makamantansu.

Sai dai, daga bisani shafukan sun dawo aiki, tare da kawar da dukkannin matsalolin da aka fuskanta kusan sa’a guda.

Ba kuma wannan ne karo na farko, da shafukan su ka taɓa tsayawa ba, domin idan mai bibiyar Rariya Online zai iya tunawa, a baya ma shafukan Facebook, Instagram da WhatsApp sun taɓa tsayawa kusan sa’o’i 6 a faɗin duniya, wanda hakan ya tilastawa masu amfani da kafar WhatsApp da dama komawa zuwa Telegram, domin cigaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button