Siyasa

Yanzu-yanzu : Shugaban NNPP Na Ƙasa Ya yi Murabus

Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Farfesa Rufai Alkali, ya sauka daga kan kujerarsa.

Alkali, wanda ya bayyana ɗaukar wannan mataki ta cikin wata wasiƙa da ya aikewa Sakataren Jam’iyyar na ƙasa, ya ce ya yi hakan ne domin bawa sababbin hannu su ma damar zuwa su bawa jam’iyyar tasu gudunmawar.

Inda ya yi wa wasiƙar ta ke da, ”Takardar Sauka daga matsayin Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙasa”, ya kuma ɗora da cewar, ”Na rubuta wannan wasiƙa ne, domin bayyana maka cewar na sauka daga shugabancin jam’iyyar NNPP, daga yau, Juma’a, 31 ga watan Maris, na shekarar 2023.

”Hakan kuma ya zo ne, bayan gudanar da manyan zaɓukan ranar 25 ga watan Fabrairu, da 18 ga watan Maris, na 2023, ina kuma kyautata zaton cewar jam’iyyarmu ta NNPP ta na da kyakykyawar goben da zata zama zakara a cikin dukkannin jam’iyyun siyasa, har kuma ta lashe zaɓen shugabancin ƙasa, da sauran zaɓuka, a shekarar 2027.”

”Domin cimma wannan muradi namu, dole ne mu zurfafa tunani, mu kuma yi tsare-tsare. Kuma yanzu ne lokacin. Jam’iyyarmu ta NNPP ta na buƙatar sauye-sauye a dukkannin matakai, domin sake ƙarfafarta, da ma haɓɓaka ayyukanta, harma da ɗagata zuwa matsayin da zata shallake sauran jam’iyyun siyasa 17 da ke da rijista da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa.

”Tunda hakane, fatanmu mu kawo sabuwar Najeriya, tare da bunƙasa ta, bisa Jagorancin, Maigirma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, na tabbata babu wata sadaukarwa da ɗayanmu zai yi, a ce ta yi yawa.

”Na kuma yarda da tsarin nan na sauyi ya fara daga kaina. Hakan ne ya sanya na yanke hukuncin sauka daga kujerarata ta shugabancin jam’iyya, domin bawa sababbin hannu damar karɓa su ɗora da tasu gudunmawar. Ina fatan su yi abinda ya fi nawa.

”Ka zalika dai, a wannan wasiƙa, ina son na sanar da Jagoran wannan jam’iyya, Rabiu Musa Kwankwaso, da kwamitin zartarwarta, da ma dukkannin membobin jam’iyyar na faɗin ƙasa cewar, zan cigaba da kasancewa mamba a wannan jam’iyya ta mu, na kuma yi alƙawarin bada dukkannin wata gudunmawa, dan bunƙasar wannan jam’iyya, a kowanne mataki”.

Ya kuma yi godiya ta musamman ga Jagoran jam’iyyar na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, da Mataimakin ɗan takarar shugabancin ƙasa, Bishop Isaac Idahosa, sai shugaban kwamitin amintattu, Chief Boniface Aniebonam, da Sakataren Kwamitin, Buba Galadima, da ma membobin kwamitin zartarwa na ƙasa, da Gwamnoni, tare da ƴan majalissar tarayya, da na jihohin jam’iyyar, sai kuma dukkannin membobinta da ke faɗin ƙasa, saboda fatan alkairinsu, goyon baya, da ma ƙarfafa gwuiwa, a lokacin shugabancinsa.

”Ina addu’ar Allah ya saka muku da Alkairi. Ya ƙarawa jam’iyyar NNPP nisan kwana. Ya kuma albarkaci Najeriya”.

Kuma wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan Alhamis, 31 ga watan Maris, an aike da kwanfinta ga Jagoran jam’iyyar na ƙasa, kuma ɗan takararta na shugabancin ƙasa, a zaɓen da ya gabata, Rabi’u Musa Kwankwaso; sai shugaban kwamitin amintattu, Boniface Aniebonam, da Sakataren kwamitin amintattu, Buba Galadima.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button