Yanzu-Yanzu: Sufeto Janar Ya Sanar Da Sauya Kwamishinan Ƴan Sandan Imo, Kwanaki Kaɗan Bayan Dukan Shugaban NLC
Sufeto Janar na rundunar ƴan sandan ƙasar nan, Kayode Egbetokun, ya sanar da sauya Kwamishinan rundunar na jihar Imo, Stephen Olanwareju.
Ɗaukar wannan mataki kuma, na zuwa ne ya yin da ya rage ƙasa da mako guda a gudanar da zaɓen Gwamnonin jihohin Imo, Bayelsa da Kogi, wanda zai gudana, a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
“Ina sane da zarge-zargen da aka dinga samu akan Kwamishinan ƴan sandan jihar Imo, ta kafafen sada zumunta, amma saboda zaɓen nan za mu sauya Kwamishinan ƴan sandan Imo”, a cewar IGP Kayode, ya yin zantawarsa da tashar talabijin ta Channels, ranar Lahadi, kan tsare-tsaren da hukumar ke da su, na tabbatar da tsaro a ya yin zaɓen da ke tafe.
Idan za a iya tunawa dai, ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, NLC, ta zargi rundunar ƴan sandan jihar Imo da lakaɗawa shugabanta, Joe Ajaero, dukan kawo wuƙa, a makon da ya gabata, ya yin da ya halarci jihar domin jagorantar zanga-zangar ƴan ƙwadago, duk kuwa da yadda rundunar ƴan sandan jihar ta sanar da haramta zanga-zangar.
Kan wannan batu kuma, IGP ɗin ya ce, sauya Kwamishinan ba zai tagaza wani abu kan halin da ƙungiyoyin ƙwadagon ke ciki ba, kawai dai za a yi hakan ne, domin neman maslaha.
Muna tafe da ƙarin bayani…..