Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Dawo Najeriya, Bayan Kai Ziyarar Aiki Ƙasar Qatar
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya, bayan ziyarar kwanaki biyu, da ya kai zuwa ƙasar Qatar.
Jirgin da ke ɗauke da shugaban ƙasar, mai lamba NAF 001, ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama ba Nnamdi Azikiwe ne da misalin ƙarfe 7 na daren yau (Litinin).
Ziyarar tasa zuwa Qatar kuma, ita ce ta 12 da ya kai zuwa ƙetare, tun bayan ɗarewarsa karagar shugabancin ƙasar nan watanni tara da su ka gabata, ya kuma shafe tsawon kwanaki 75 a ƙasashen ƙetaren da ya halarta.
A ya yin dawowar tasa zuwa Najeriya kuma, shugaban ya samu tarba daga manyan muƙarraban gwamnati, da su ka haɗarda: Mataimakinsa, Kashim Shettima; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume; Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike; Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje; da shugaban rundunar tsaron farin kaya, Yusuf Bichi, da sauransu.