Kimiyya Da Fasaha
Yanzu-Yanzu: WhatsApp Ya Ƙaddamar Da Tsarin Channels
Kamfanin Meta, wanda ke da mallakin Manhajojin Facebook, WhatsApp, Instagram, Messenger, da ma Threads, ya sanar da ƙaddamar da tsarin tashoshi (Channels) akan Manhajar WhatsApp.
Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg, shi ne ya sanar da ƙaddamar da tsarin Channels ɗin, a yau (Laraba), inda ya ce za a iya cin karo da wannan sabon tsari, idan aka sauke sabuwar Manhajar WhatsApp.
“A yau mun fara ƙaddamar da Channels na faɗin duniya, akan manhajar WhatsApp, inda muka sanya dubunnan Channels, da za ku iya bi, a WhatsApp ɗin.
“Za ku iya gani da samun Channels ɗin ne, a sabuwar Manhajar WhatsApp, ta hanyar danna maɓullin ‘Updates’.”, A cewarsa.