Yaran Ƴan Gudun Hijira 1,200 Sun Rasa Rayukansu, A Sudan
Sama da yaran ƴan gudun hijira 1,200 da ke ƙasa da shekaru biyar ne su ka rasa rayukansu, a ƙasar Sudan, a tsakanin 15 ga watan Mayu, zuwa 15 ga watan Satumban shekarar damu ke ciki, a sansanoni daban-daban, sakamakon ƙyanda, da ƙarancin ingantaccen abinci.
Sansanin ƴan gudun hijira na Um Sangour, da ke Kosti a kudancin ƙasar kaɗai, na marabtar dubban masu gudun hijira.
Rikicin ƙasar Sudan, wanda ya riski wata na biyar kuma, na daga cikin abubuwan da su ka taɓarɓara fannin lafiyar ƙasar, sakamakon ƙarancin maáikata, ƙarancin kayayyakin ceton rayuka, da sauran manya-manyan dalilai.
A jiya ne dai, mai magana da yawun ƙungiyar UNICEF, ya bayyana cewar, hukumar ta karɓi kimanin dalar Amurka miliyan 838, kwatankwacin Euro miliyan 784, domin taimakon yara miliyan 10, da ke ƙasar Sudan.
Shaánin kiwon lafiya a ƙasar, na cikin tsaka mai wuya, sakamakon rahotannin ƙarancin ingantaccen abinci, ɓarkewar cututtuka, da ma ƙarancin magunguna da wutar lantarki, tare da ruwan sha.
UNICEF ɗin ta kuma yi hasashen yadda dubban jariran ƙasar za su rasa rayukansu, daga yanzu zuwa ƙarshen shekarar da mu ke ciki, a sakamakon taɓarɓarewar shaánin lafiya.