Zamantakewa

Yaro Mai Shekaru 14 Ya Hallaka Mahaifiyarsa, Tare Da Harbin Bazawarinta Har Karo 5

An kama wani yaro, mai shekaru 14 a duniya, a Riverview, da ke Florida, bayan da ya hallaka Mahaifiyarsa, tare da harbin saurayinta har karo biyar.

Bazawarin Mahaifiyar, mai suna, Chronister, a ya yin zantawarsa da Manema Labarai a daren ranar Asabar, ya bayyana cewar yaron ya sanya bindiga ne, akansa, inda ya yi ta harbinsa har karo biyar.

Bayan mintuna 16 kuma, sai wannan Matashi ya yi saranda, tare da mayar da bindigar zuwa nasa kan, da zummar sheƙe kansa da kansa.

Daga nan ne kuma, sai Jama’a su ka yi tara-tara, tare da fisge bindigar daga hannunsa. Bayan nan kuma, ya cigaba da yunƙurin fizgeta, Amma abin yaci tura, har sai da Jami’an rundunar ƴan sanda su ka harbe shi a hannu.

A nan ne kuma, matashin yaron ya yi kan Jami’an, inda su ka yi amfani da damar wajen tasa ƙeyasarsa zuwa komarsu.

Jami’an ƴan sanda sun samu wancan mutum baligi, wanda bazawari ne ga Mahaifiyar Yaron dai, Kwance a cikin jini, ɗauke da harbin bindiga a hannaye da fuskarsa.

A gefe guda kuma, aka tsinci gawar Mahaifiyar Yaron, wacce ake kyautata zaton yaron ne ya harbeta a ya yin da ya ke yunƙurin harbin nata Bazawarin.

Yayan wannan matashi mai ta’asa dai, ya bayyana cewar, ya na ɗaki a lokacin da ya ji Mahaifiyarsu ta na cacar baki da Bazawarin nata. Mintuna kaɗan bayan hakan kuma sai ya ji ƙarar harbin bindiga, inda ya yi sauri ya fito daga ɗakinsa domin ganin me ke faruwa. Ya na fitowa kuma, sai ƙanin nasa ya harbe shi da bindiga shi ma, mmma ya yi nasarar tsere mata.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button