Kimiyya Da Fasaha

Yawan Amfani Da Waya, Yana Haifar Da Ƙarancin Maniyyi

Rahoton wani bincike da masana kimiyya su ka gudanar, a ƙasar Switzerland, ya gano yadda yawaitar amfani da wayar salula ga al’umma ke haifar musu da ƙarancin ruwan maniyyi.

Amfani da wayar salula sau 20 ko fiye da haka, ga Matasan da ke tsakanin shekarun balaga na 18 zuwa 22, a kowacce rana, shi ne babban ma’aunin da ke bayyana haɗarin yiwuwar samuwar ƙarancin maniyyin a jikinsu, a cewar binciken.

Masana dai, sun daɗe su na bayyana cewar, gudanar ruwan maniyyin na da alaƙa da kwanciyar hankalin ƙwaƙwalwa, don haka duk lokacin da aka takura mata, ta hanyar amfani da waya, to gudanuwar maniyyin kan ja baya.

Maniyyi, wani ruwa ne mai kauri da Ubangiji ke halitta a jikin bayinsa waɗanda su ka kai matakin shekarun balaga, domin basu damar hayayyafa ta hanyar fitarsa, a duk lokacin da hashafa ta ɓuya a cikin kafa, ko kuma aka yi amfani da wasu dabaru wajen fitar da shi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button