Yawan Yin Wanka Na Da Matuƙar Illa Ga Fatar Jiki – Binciken Masana
A ya yin da yanayin sanyi ke ƙara kankama a yankin Arewacin Najeriya, Jaridar Rariya Online ta yi katarin zaƙulo muku sakamakon wani binciken masana lafiya, wanda ya gano ɗumbin Illolin da ke tattare da yawan yin wanka.
Wani ƙwararre, mai suna, Mathew daga Cibiyar nazarin lafiyar fata ta Naik, shi ne ya gabatar da sakamakon binciken, wanda Jaridar The Sun ta wallafa.
Binciken dai, ya gano cewar, fata na da wasu muhimman sinadarai, da ke ƙara mata lafiya, waɗanda yawan yin wankan ke wanke su.
Bugu da ƙari wanka na haifar da cututtuka irinsu, Bushewar Fata; Ƙaiƙayi, da ma fashewar fatar, wanda ke bawa cututtuka da dama lasisin shiga jikin ɗan Adam.
Har wa yau kuma, wani bincike ya gano cewar, kaso 80 na al’ummar da ke rayuwa a ƙasashen China da Amurka, su na yin wanka ne sau biyu, ko sau uku kacal a mako guda.
Ka zalika, wani binciken na daban, da Mujallar Clinical Microbiology ta gudanar, ya gano cewar, yin wanka sosai ya fi komai Illa, musamman ma, bayan an yi aski, domin cututtuka na samun damar shiga ta hanyar sabon gashin da aka yanke.
Rahoton binciken ya ƙara da cewa, sosunan wanka na ɗaukar cututtuka ne, bayan an gama wanka da su an ajiye.
Sai dai, wasu daga cikin Likitoci na ganin cewar, yawan yin wankan na gyara fata, tare da garkuwar jiki, lamarin da da dama daga cikin masana lafiyar fata su ka musanta.