Labarai

Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano, Ya Naɗa Sabon Sakataren Yaɗa Labarai

Zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin fitaccen Ɗan Jaridar nan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a matsayin Sakataren yaɗa labaransa.

Naɗin nasa kuma, na ɗauke ne ta cikin wata wasiƙa, da ke ɗauke da sa hannun Shugaban Kwamitin karɓar kujerar Gwamna, da aka fitar, ranar Alhamis, a madadin zaɓaɓɓen Gwamnan.

Wasiƙar ta kuma ce, an naɗa Sunusi Dawakin Tofa, a wannan muƙami ne, saboda cancantarsa, gaskiya, da ma jajircewarsa wajen yin aiki tuƙuru, wanda ya zame masa linzami tun shekarar 2019.

Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, Sunusi Dawakin Tofan ya kasance mai magana da yawun zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kanon, a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ka zalika, ya na da ƙwarewa matuƙa a fannin yaɗa labarai, bayan da ya samu gogewar aiki har ta shekaru 19, a ƙasa, ƙasa da ƙasa, da ma kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.

Ka zalika, ya taɓa lashe kambun Ɗan Jarida mai binciken ƙwa-ƙwaf na Cambridge Education, a shekarar 2008.

Ya kuma samu Digirinsa na farko, a fannin Aikin Jarida (Mass Communication) ne, a Jami’ar Maiduguri, inda ya kuma yi Digirinsa na biyu, a Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola, da ke Ogbomosho, a jihar Oyo, ya kuma ƙara wani Digirin na Biyu, kan hulɗa da Jama’a (Public Relations) a Jami’ar Bayero, da ke Kano.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button