Zaɓen Kano: Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar INEC Da NNPP Na Korar Ƙarar APC Cikin Gaggawa
Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar Kano, ta yi watsi da buƙatar da Lauyoyin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), jam’iyyar NNPP, da ma zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, su ka miƙa a gabanta, su na buƙatar ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar gabanta, ta na ƙalubalantar nasarar da NNPP ta samu a zaɓen Gwamnan jihar da INEC ta gudanar, a watannin farkon wannan shekarar, inda Kotun tace wajibi ne ta yi bayani dalla-dalla.
Zuwa yanzu kuma, Kotun ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe guda biyu, daga cikin uku da jam’iyyar ta APC ta shigar a gabanta, bayan da ta fara da tabbatar da sahihancin kasancewar Abba ɗan jam’iyyar NNPP, wacce ya yi takara a ƙarƙashin tutarta.
Kotun sauraron ƙarar zaɓen kuma, na yanke hukunce-hukuncen nata ne a yau, kaitsaye ta Manhajar Zoom, bayan da Alƙalai su ka gaza halartar Kotun a zahiri, bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba.