Za a Daina Shigo Da Man Fetur Najeriya A Watan Disamba
Kamfanin Mai Na Ƙasa (NNPCL), ya bayyana cewar, zai daina shigo da tataccen ɗanyen manfetur cikin ƙasar nan, a watan Disambar 2024, ya yin da dukkannin matatun mai na ƙasa su ka dawo aiki.
Ya kuma ƙara da cewar, fannin man ƙasar nan, zai bunƙasa yawan kuɗaɗen shigar da ya ke samarwa zuwa Naira tiriliyan 4.5 zuwa ƙarshen shekarar da mu ke ciki ta 2023, ya na mai wuƙar ƙugu da cewar, za a kammala aikin matatar manfetur ta Fatakwal da kamfanin ya ke jagoranta, a watan na Disambar wannan shekara.
Shugaban gungun kamfanin na NNPCL, Mele Kyari, shi ne ya bayyana hakan, ranar Alhamis, ya yin da ya jagoranci tawagar masu ruwa da tsakin kamfanin, zuwa tattaunawa da Shugaban Majalissar Wakilai ta ƙasa, Tajudeen Abbas, inda shugaban Majalissar ya miƙa buƙatar ganin an cefanar da matatun man ga ƴan kasuwa.
Su ma dai, ƴan kasuwar manfetur, sun bayyana ƙwarin guiwa, kan yiwuwar kammala aikin matatar manfetur ɗin ta Fatakwal, tare da fara aikinta, zuwa watan Janairun 2024, su na masu bayyana yadda hakan zai taka gagarumar rawa wajen zaftare farashin kayayyakin da ke da alaƙa da Albarkatun manfetur.
A ya yin ganawar tasu, wacce ta gudana, a babban birnin tarayya Abuja, Kyari, ya ce a halin yanzu Najeriya ta ɗauki hanyar daina shigo da tatattun albarkatun manfetur zuwa 2024, kuma ya na mai kyautata zaton ma za a ayyana Najeriyar a matsayin guda daga cikin ƙasashe mafiya fitar da tataccen manfetur ɗin, dukka a shekarar ta 2024 da za mu shiga.
Kyari ya kuma ƙara da cewar, dukkannin matatun manfetur na Fatakwal, Warri, da Kaduna, za su dawo cikakken aiki nan gaba kaɗan.
Ya kuma bayyana tallafin manfetur a matsayin babban abin da ya hana gyaruwar matatun man, tun tsawon shekaru, ya na mai bayyana yadda cire tallafin ya karkato da hankulan masu sanya hannayen jari daga ɓangarori daban-daban.