Za a Dinga Aikewa Da Buƙatar Neman Bashin Ɗalibai Ta Online, Ya Yin Da Ake Sa Ran Fara Gudanar Da Shirin A Janairun 2024
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbabiamila, ya bayyana cewar, tuni shirye-shirye su ka yi nisa, dan fara gudanar da shirin bawa Ɗaliban manyan makarantu bashin kuɗaɗen karatu, daga watan Janairun 2024.
Gbabiamila, ya bayyana hakan ne, ranar Juma’a, a jihar Lagos, ya yin da ya ke gabatar da muƙala mai taken, “Tallafar Matasan Najeriya, A Halin Matsin Tattalin Arziƙin Da Aka Tsinci Kai”, a ya yin bikin yaye ɗaliban Kwalejin Fasaha ta YABATECH, karo na 35.
Gbabiamila ya kuma ce, domin sauƙaƙa tsarin, masu neman rancen za su dinga cikewa ne ta yanar gizo (Online), za kuma a tantance su ta Online ɗin, sannan a saka musu kuɗin bayan tabbatar da sahihancin bayanan su ka shigar”.
Ka zalika bayyana yadda “A farkon wannan shekarar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu akan dokar bayar da bashin karatun na Ɗalibai maras ruwa. Ana kuma cigaba da shirye-shiryen ganin tsarin ya fara aiki a watan Janairun 2024, domin Ɗaliban Najeriya su samu bashin, kuma su biya kuɗaɗen karatunsu. An kuma tsara shirin ne ba tare da wani shinge tsakanin mai bayarwa da masu karɓar bashin ba. Ɗaliban da su ke buƙata za su cike ne Online, a tantance su a Online, a kuma tura musu kuɗaɗen. Ba a buƙatar sai kasan wani domin ka samu damar amfana da shirin, tsari ne za a yi shi na gaskiya da gaskiya”.
A nasa jawabin na daban, shugaban Kwalejin Dr. Ibraheem Abdul cewa ya yi, Kwalejin ta mayar da hankali ne wajen tallafar matasa ta hanyar ɓullo da shirye-shirye daban-daban.