LabaraiUncategorized

Za a Fara Biyan Masu Hidimar Ƙasa Naira 85,000 A Jihar Taraba

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya amince da fara biyan dukkannin masu hidimar ƙasar da aka tura zuwa makarantun jihar, Naira Dubu Hamsin-Hamsin a matsayin alawus ɗin kula da lafiya.

Kwamishiniyar yaɗa labaran jihar, Zainab Usman, ita ce ta bayyana hakan, ta cikin wani jawabi da ta fitar, a ranar Lahadi.

Ta kuma ce, Gwamnan ya amince da biyan ƙarin Naira 25,000 ga dukkannin masu hidimar ƙasar, a matsayin alawus ɗin wuraren zama, da ma tallafin Naira 10,000 ga kowannensu, daga Gwamnatin jihar.

Kwamishiniyar ta ce, Gwamnan ya amince da hakan ne, duba da ƙarin shiga makarantu da ake samu, sakamakon tsarin karatu kyauta da Gwamnatin jihar ta bijiro da shi, a Makarantun Firamare da Sakandire, tare da raba Kayan Makaranta, da sauran kayan koyo da koyarwa.

Kwamishiniyar ta ƙara da cewar, Gwamnan ya umarci ma’aikatar Ilimi da ta Matasa da Cigaban Wasanni ƙarƙashin Kwamishinoninsu, da su tabbatar da aiwatar da sababbin matakan da Gwamnatin jihar ta amince da ɗauka.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button