Za a Fara Biyan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi A Watan Afrilu
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar, za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata, a ranar 1 ga watan Afrilun 2024.
Ministan yaɗa labarai, Idris Mohammed ne, ya bayyana hakan, ta cikin wata tattaunawa a babban birnin tarayya Abuja, ya na mai cewar wa’adin mafi ƙarancin albashi na Naira 30,000 da ake amfani da shi a yanzu, zai kawo ƙarshe ne, a ƙarshen watan Maris ɗin 2024.
Mohammed, ya bayyana hakan ne, ranar Alhamis, a ya yin da ya ke ƙarin haske kan fuskokin da kasafin kuɗin 2024 zuwa 2026 za su kalla, ya na mai cewar, Gwamnatin tarayya za t kashe kimanin Naira tiriliyan 24.66 wajen biyan Albashin ma’aikata, a shekarun 2024, 2025, da 2026.
Biyo bayan cire tallafin manfetur da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne dai, Gwamnatin tarayya ta amince da biyan ma’aikata ƙarin Naira 35,000 a matsayin tallafin rage raɗaɗi.
Tuni kuma, gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago su ka bayyana cewar, ƙarin Albashin na wucin gadi ne, za a yi tabbataccen ƙarin Albashi ne, a shekarar 2024.