Za a Fara Kama Iyayen Yara Masu Talla
Gwamnatin jihar Anambra, ta ce dukkannin Iyayen da yaransu ke gararambar talla, ko yin bara a bakin tituna, su na cikin haɗarin shiga hannun hukuma, da ma gurfana a gaban kuliya.
Kwamishiniyar Mata da walwalar al’umma, ta jihar, Mrs lfy Obinabo, ita ce ta bayyana hakan, a ya yin da ta ke jawabi, a ranar Iyali ta Duniya, ta na mai cewar ɗaukar matakin zai taka muhimmiyar rawa wajen rage yadda ɗabi’ar ta talle, da roƙo ke cigaba da ƙaruwa, a jihar.
Ta kuma ce, hakan zai kasance wani shinge da za a kallafawa Iyaye da ma sauran masu alhakin lura da yara.
Ta kuma ce, Ma’aikatarta za ta cigaba da zaburar da Iyaye wajen ganin sun sanya yaransu a makaranta, ta na mai cewar hakan ita ce hanya ɗaya tilo ta kawo karshen fatara da talauci.
”Yaran nan su na buƙatar a nuna musu So, ƙauna, Kulawa, da ma girmama buƙatunsu, ba wai cutarwa, ko zaluntar su da ayyukan gida ba” – a cewarta.