Za a Fara Rubuta WAEC Ta Hanyar Na’ura Mai Ƙwaƙwalwa
Hukumar shirya jarrabawar kammala Makarantun Sakandire, ta ƙasashen yammacin Afirka (WAEC), ta bayyana cewar, shirye-shirye sun yi nisa na fara rubuta jarrabawar ta hanyar amfani da na’ura maiƙwaƙwalwa.
Shugaban Ofishin hukumar na ƙasa, Mr Patrick Areghan, shi ne ya bayyana hakan, a ya yin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ranar Asabar, a birnin Lagos.
Areghan kuma, na yin waɗannan kalamai ne, a ya yin da ya ke bayyana ɗumbin nasarorin da ya cimma a hukumar, tun bayan ɗarewarsa karagar Shugabancinta, ya yin da ya ke shirye-shiryen bankwana a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa.
Hakan kuma, shi ne zai kawo ƙarshen wa’adinsa na tsawon shekaru Uku, da ya shafe ya na Shugabantar hukumar.
Areghan ya kuma ce, fara gudanar da jarrabawar ta hanyar amfani da na’ura maiƙwaƙwalwa (CBT), na daga cikin shirye-shiryen hukumar na nan kusa.
“Mun fara wani abu na shirye-shiryen fara rubuta jarrabawar a Kwamfiyuta. Mun ma yi nisa a shirin, domin Magatakardan hukumar ma ya na yin iya bakin ƙoƙarinsa.
“Amma hakan ba shi da sauƙi irin yadda wasu mutanen su za su zata. Hakan kuma ba ya rasa nasaba da tambayar kanmu da mu ke yi, shin ta yaya za mu gudanar da CBT a jarrabawoyin Practicals da Essay ?.
“A halin da ake ciki, tambayoyin Objectives kawai za mu iya. Amma mutane da dama ba za su kalli abin ta wannan fuskar ba. Za su ƙalubalance mu da cewar ai wasu suna yi, meyasa WAEC ma ba za ta yi ba ?.
“A yanzu, babu wanda zai yi batu kan wutar lantarki; Makarantu nawa ne ma su ke da ƙwarewa a fannin na’ura maiƙwaƙwalwar ?, Guda nawa ne kuma su ke da na’urorin tare da wadatacciyar wutar lantarkin da za ta ɗauke su ?.
“Ko da su na da dukkannin waɗannan abubuwan ma, ya za ka yi da wancan ƙalubalen na jarrabawoyin Theory da Practical ?, Saboda haka waɗannan su ne matsalolinmu, kuma shi ne abinda nake fatan hukumar ta magance a nan kusa.
“Za mu iya gudanar da jarrabawar nan ta CBT, ko da dai za mu fara da sashen tambayoyin Objectives ne kawai”, a cewarsa.