Kasuwanci

Za a Kammala Aikin Layin Dogon Kano Zuwa Maraɗi A Shekarar 2025 – Minista

Ministan Sufuri, Sanata Saidu Ahmad Alƙali, ya tabbatar da cewar, za a kammala aikin titin jirgin ƙasan Kano zuwa Maraɗi a shekarar 2025.

Alƙali ya bada wannan tabbaci ne, ranar Juma’a, a Katsina, ya yin da wani zagayen duba yadda aikin wanda zai laƙume kimanin Dalar Amurka Biliyan 2, da tsohuwar Gwamnatin Buhari ta bayar, ya ke gudana.

Ministan ya kuma bayyana gamsuwarsa da yanayin da aikin ya ke ciki, inda ya ce Aikin da ake gudanarwa na Earthwork ya doshi kaso 80 na kammalawa, inda kuma za a fara Aikin shimfiɗa layin gogon da zarar an kammala Earthworks.

A nasa ɓangaren, Babban Jami’in Aikin, Mr. Vladislav Bystrenko, ya ce Aikin zai laƙume kimanin Dalar Amurka biliyan 1.95 ne, kamar yadda Kwantiragin da Gwamnatin tarayya ta rattaɓawa hannu a shekarar 2021 ya nuna.

Ya kuma ce, sun fara tsare-tsaren gudanar da aikin tun kafin Gwamnatin tarayya ta sakar musu kuɗaɗen.

Mr. Vladislav Bystrenko, ya kuma ce Gwamnati na cigaba da sanya himma wajen ganin an kammala aikin a shekarar 2025 ɗin da aka sanya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button