Za a Maka Gwamnatin Kano A Gaban Kotu, Saboda Yin Rusau
Kamfanin da ke aikin gina sabon Hotel ɗin Daula, Lamash Properties Limited, ya sha alwashin maka gwamnatin Kano a gaban kotu, tare da buƙatar ta biya shi diyyar Naira biliyan 10 da ya kashe a ya yin ginin Hotel ɗin, wanda Gwamnati ta jagoranci rushewa.
A daren Lahadi ne dai, Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagoranci, Abba Kabir Yusuf, ta ƙaddamar da rushe ginin Hotel ɗin na Daula, wanda ake ganin ya lashe biliyoyin Nairori, bisa zargin mallakar wurin ta haramtacciyar hanya.
Tun a shekarar 2020 ne dai, tsohuwar Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan wancan lokaci, Abdullahi Umar Ganduje, ta gayyaci kamfanin na LAMASH Properties Limited, da sauran takwarorinsa, wajen haɗa hannu, domin farfaɗo da tsohon Hotel ɗin na Daula, a tsarin PPP.
Kuma wata sanarwa da kamfanin ya fitar, a ranar Lahadin da ta gabata, ta bayyana yadda kamfanin ya mallaki shiyyar Hotel ɗin ta halastacciyar hanya.
Idan ba a manta ba kuma, a ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata ne, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci ƙaddamar da Hotel ɗin.
Sai dai, wani babban abin mamaki da ya faru, a cewar sanarwar da kamfanin ya fitar shi ne, kiran da kamfanin ya samu da misalin ƙarfe 2 na daren Lahadi, 4 ga watan Yunin 2023, inda kuma aka bayyana musu cewar, Gwamnatin ta Kano, ƙarƙashin jagorancin, Abba Kabir Yusuf ta rushe ginin wurin nasu, ta hanyar amfani da Motocin rusau (bulldozers), inda abubuwan da aka rushe su ka haɗar da, Ginin Ajujuwa kimanin 90, Sai sassan sayar da kaya (Boutique) guda 5, da ma sashen saye da sayarwa (malls) wanda aka kammala kaso 90 na Aikinsa, da ma ɓangaren saukar baƙi.
Sanarwar ta kuma ce, abin da Gwamnatin ta Aikata, abu ne da zai ƙara ta’azzara matsalar rashin Aikin yi, da ma sauran matsaloli.
”Kuma babu wani ɓangare daga Gwamnati da ya nemi tattaunawa da mu domin warware yadda mu ka mallaki wannan wuri.
”Dama mun faɗa mu ba sayen wurin nan mu ka yi ba, amma mun bi hanya ta doka wajen mallakarsa. Abin da Gwamnati ta Aikata abin kunya ne, kuma abu ne da zai sanya tsoro a zuƙatan masu sha’awar zuwa su sanya hannayen jari, a wannan jiha.
”Saboda haka mun umarci tawagar Lauyoyinmu da su shigar da Gwamnati ƙara kan wannan abu da ta Aikata, tare da buƙatar ta biya mu diyyar Naira biliyan 10, wacce muka kashe a Aikin wurin, a kuma dakatar da Gwamnatin daga ɗaukar dukkannin wani mataki da zai yi wa tsarin namu na PPP karantsaye, ko kawo masa cikas.”