Za a Rabawa Ƴan Ƙungiyar Ƙwadago Motocin Shinkafa Biyu, A Niger
Gwamnan Jihar Niger, Umaru Bago, ya amince da raba manyan motocin Shinkafa Biyu, masu ɗauke da buhunhuna masu nauyin 50kg ga membobin ƙungiyar ƙwadago, reshen Jihar, a matsayin wani sashe na rage musu raɗaɗin janye tallafin manfetur.
Bago, ya bayyana amincewar tasa ne, a ya yin wani taron walima da aka shirya, na ƙaddamar da sabon Ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar, Yakubu Garba, da aka gina, a birnin Minna.
Ya kuma ce, an amince a bawa ƙungiyar ta NLC kimanin Naira miliyan 110 domin aikin sanya Ido kan rabon kayan tallafin a mazaɓun jihar, kimanin 274.
Gwamnan, ya kuma buƙaci ƙungiyar da ta janye Yajin Aikin gargaɗin kwanaki biyun da ta ke tsaka da gudanarwa.
A nasa jawabin, Yakubu Garba, godewa Gwamnan ya yi, kan aikin da ya ke gudanarwa ba dare – ba rana, wajen ganin an ciyar da Jihar gaba.