Za a Rufe Rijistar DE A Nan Kusa – JAMB
Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa, JAMB, ta buƙaci dukkannin ɗaliban da ke da sha’awar yin rijistar tsarin shiga Jami’a kaitsaye (DE) da su gaggauta yin hakan.
JAMB, ta yi wannan kira ne, ranar Juma’a, ta cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X.
Inda hukumar tace ana cigaba da rijistar DE ɗin, amma ana gab! da rufewa.
“Kira ga Ɗaliban DE na shekarar 2024!
Muna sanar da Ɗaliban da har yanzu basu kammala rijistarsu ba cewar, ana cigaba da rijista, amma an kusa rufewa. Saboda haka dukkannin waɗanda su ka ga wannan sanarwa, akwai buƙatar su kammala rijistarsu, tun lokaci bai ƙure ba”, a cewar saƙon.
Idan za ku iya tunawa dai, hukumar ta JAMB ta ɗage lokacin rufe rijistar DE har zuwa lokacin da bata bayyana ba, bayan da a baya tace za ta rufe rijistar a ranar 28 ga watan Maris, inda ta ƙara ɗage lokacin zuwa ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata.