Labarai

Za a Samar Da Ofisoshin Ƴan Sanda A Rumbunan Abincin Abuja

Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya Abuja, Dr. Mariya Mahmoud, ta bayyana cewar, Gwamnatin Abuja za ta samar da Ofisoshin ƴan sanda, a dukkannin rumbunan adana abincinta, domin gujewa haikewa wuraren, tare da kwashe kayayyakin da aka adana a ciki.

Dr. Mariya, ta bayyana hakan ne, ranar Litinin, a babban birnin tarayya Abuja, bayan ta kai ziyara rumbun adana kayan abinci da ke Gwagwa- Tasha, wacce wasu fusatattun ƴan Najeriya da ke cikin halin yunwa su ka kaiwa farmaki a ranar Lahadi, tare da kwashe kayayyakin abincin da ke ciki.

Ministar, ta kuma bayyana fasa rumbun a matsayin babban abin damuwa, tana mai cewar ɓata garin da su ka fasa rumbun sun kwashe hatsi, da sauran kayayyakin abincin da ke ciki, harma da kwanukan rufi.

Bugu da ƙari, ta bayyana cewar lamarin ya zarce ace yunwa ce ta jawo shi; kawai dai ta’addanci ne.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button