UncategorizedZamantakewa

Za a Sanya wa Zawarawan Da Gwamnatin Kano Za Ta Aurar Sadakinsu, Ta Asusun Banki

Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin Jagorancin, Abba Kabir Yusuf, ta umarci da a sanyawa Mata 1,800 da za ta yi wa Auren Gata kuɗaɗen Sadakinsu, kimanin Naira Dubu Hamsin-Hamsin, a Asusunsu na Bankuna.

Shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shi ne ya bayyana hakan, ya yin da ya ke zantawa da kafar rediyon Nasara, a ranar Talata.

Malamin ya kuma ce, Gwamnatin Kanon ta ware kimanin Naira miliyan 90 ne, domin bayar da kuɗaɗen sadakin, inda kuma ta ware Naira miliyan 22, domin bayar da dubu 500 ga ƙananan hukumomi, dan su gudanar da bikin walimar Auren.

Ka zalika, za a raba Naira Dubu Ashirin-Ashirin ga dukkannin Matan, a matsayin Jari (Jimilla Naira miliyan 36), dan ganin sun rungumi Sana’o’in dogaro da kai.

Sannan za a bawa kowanne Ango da Amarya Buhun Shinkafa (mai 50), Katan ɗin Macaroni, da Jarkar Mai a matsayin Gara.

An dai zaɓo Mata Da Maza Talatin-Talatin ne, daga ƙananan hukumomin da ke wajen birnin Kano, ya yin da aka ɗauko Hamsin-Hamsin daga ƙananan hukumomin cikin birni, domin shigar da su cikin wannan tsari.

Sheikh Daurawa, ya kuma ce, sun so ganin an gudanar da wannan bikin Aure kafin cikar Gwamna kwanaki 100 akan karagar mulki, sai dai mataka 50 ɗin da ake bi wajen tantance Ma’auratan ne su ke da ɗan tsauri, tare da ɗaukar lokaci.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button