Za a Yi Fama Da Rashin Wuta A Najeriya
Akwai yiwuwar miliyoyin masu amfani da wutar lantarki a ƙasar nan, za su tsinci kansu a cikin duhu, a ƴan makonni masu zuwa, bayan da gwamnatin tarayya, ta ƙarƙashin kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasa, da ma ƴan kasuwar wutar ta lantarki su ka fara daina bayar da wuta ga kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki, saboda yawan basussukan da ke kansu.
Wani bincike da jaridar PUNCH ta gudanar, ya gano yadda kamfanin ya fara ɗaukar wannan mataki akan wasu daga cikin kamfanonin rarraba hasken lantarkin.
MO, wanda shi ma wani rashe ne na kamfanin samar da wutar, ya sanar da kamfanonin rarraba hasken lantarkin, cewar zai fara daina basu wuta, saboda gaza biyansa kuɗaɗen wutar da ya ke binsu.
Tun bayan ɓullar waccar sanarwa kuma, tuni aka fara ganin raguwar samun hasken lantarkin a ƙasar nan, inda yankuna da dama ke ƙorafin ƙaranci, ko ma rasa wutar baki ɗaya.
Ta cikin sanarwar kwana-kwanan nan da Babban Daraktan kamfanin na MO ya fitar dai, ya buƙaci masu rarraba hasken lantarkin da su biya shi dukkannin kuɗaɗen da ya ke binsu. Hakan kuma ya zo ne, bayan tsoma bakin Ministan Makamashi, Abubakar Aliyu.
Wani binciken jaridar PUNCH dai, ya gano kamfanonin wutar lantarkin da waɗannan basussuka su ka shafa, da su ka haɗarda; Kamfanin rarraba hasken Lantarki na Abuja, na Benin, na Enugu, na Ibadan, na Ikeja, na Jos, na Kaduna, na Kano, na Fatakwal, APL na Aba, da ma Kamfanin tama da ƙarafa na Ajaokuta.
Wanda ba a bin bashi kuwa daga cikinsu shi ne, Kamfanin Wuta na Niger Delta.