Tsaro

Za a Yi Harbe-Harben Bindiga, A Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, ta bayyana cewar, Ma’aikata da Ɗaliban Kwalejin horas da Jami’an hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa (Custom), da ke Gwauron Dutse, a Kano, za su gudanar da atisayen gwajin harbin bindiga, har na tsawon kwanaki bakwai (mako guda), a Hawan Kalibawa, da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, daga yau (Litinin), 11 ga watan Satumba, zuwa Lahadi, 17 ga watan Satumban 2023, daga ƙarfe 6 na safiya, zuwa 6 na yammacin kowacce rana.

Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne, ta cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, a madadin Kwamishinan rundunar ƴan sandan jihar ta Kano.

Sanarwar ta kuma buƙaci Jama’a, musamman waɗanda ke zaune a yankunan, Dambazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum, da ma ƙauyen Dandalama, da ke ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Ungogo da kewayensu, da su ƙauracewa zuwa yankunan harbin, kuma ka da su tsorata da ƙarar harbe-harben da za su yi ta ji.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button