Za a Yi Wa Masu Buƙata Ta Musamman Rijistar JAMB Kyauta
Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB), ta bayyana cewar, dukkannin Ɗalibai masu buƙata ta musamman, da ke son rubuta jarrabawar UTME a wannan shekarar (2024/2025), za su iya rijistar jarrabawar ba tare da biyan ko sisin Kobo ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, shi ne ya bayyana hakan, da safiyar yau Litinin, ya yin da ya ke ƙaddamar da fara rijistar jarrabawar ta wannan shekarar.
“Domin tallafawa mutanen da ke da kowanne irin nau’i na buƙata ta musamman, JAMB za ta basu damar yin rijistar UTME da DE na shekarar 2024 kyauta,” a cewarsa.
Oloyede, ya kuma ce hukumar ta ɗauki dukkannin matakan da su ka dace, wajen ganin rijistar ta su ta gudana, ba tare da wata matsala ba, inda ya ce za a bawa Ɗaliban da ke da lalurar gani, Littafan da za su dinga saurara (Audio Books).
Ya kuma ce, an bada shawarar samar da littattafan na saurara ne, a ya yin taron Equal Access na ƙasa, kan Ilimi mai zurfi, da aka gudanar.