Za Mu Kare Ƴan Najeriya Daga Faɗawa Cikin Talauci – A Cewar Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya, ta bayyana cewar, ba kakkaɓe talauci ne kawai shirinta ba, tana son kare dukkannin wani ɗan ƙasar ne, daga tsunduma cikin fatara.
Ministar jinƙai da kakkaɓe talauci, Dr. Betta Edu, ita ce ta bayyana hakan ranar Juma’a, a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ya yin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu, da ta kai jihar, kamar yadda jawabin da mai bata shawara na musamman kan yaɗa labarai, Rasheed Zubair ya fitar, ya bayyana.
Ministar, wacce ta samu tarba daga Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ta ce Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin magance matsalolin da ke buƙatar agaji, domin kakkaɓe talauci a ƙasar nan, bisa burinsa na bunƙasa muradan ƙarni na 1 da na 2.
“Wannan Ma’aikata, a ƙarƙashina, ba kawai tana son magance talauci bane, a a muna son ma mu samar da matakan kare Jama’a daga faɗawa layin na talauci., a cewarta.
Ta kuma sanar da Gwamnan, irin ƙoƙarin da Gwamnatin tarayya ta himmatu da yi, wajen ganin an dawo da ƴan gudun hijirar Najeriya, zuwa gidajensu na asali, a shekarar 2024.
A nasa ɓangaren, Gwamna Zulum, ya tabbatarwa da Ministar cewa, Gwamnatinsa za ta bada haɗin kai da gudunmawa 100 bisa 100, wajen ganin an kawo ƙarshen matsalolin fatara da talauci, a Jihar ta Borno.
Inda ya ce, da zarar an kawo ƙarshen talauci, babu shakka matsalolin rashin tsaro za su zama tarihi.