Za mu So Dawowar Kwankwaso APC, Saboda Muna Buƙatar Tsayayyen Jagora – Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa
Biyo bayan fitar wasu rahotanni da ke bayyana yadda zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, kuma Jigon Jam’iyyar NNPP, da ke da mallakin kujerun shugabancin jihar Kano, ciki kuwa har da kujerar Gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso, ranar Litinin, a birnin Paris, al’umma da dama na cigaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan buƙatar da ake tsammanin Tinubun ya miƙawa Kwankwaso ta haɗuwa domin yin tafiya guda, a ƙoƙarin da ya ke cigaba da yi, na ganin ya tafi da jam’iyyun adawa, a gwamnatinsa.
Rahotanni dai, sun tabbatar da cewa, zaman tattaunawar na sa’o’i biyu, ya gudana ne, ranar Litinin, da misalin ƙarfe 12:30 na rana, Inda aka kammala da misalin ƙarfe 4:45 na yammaci. Kuma zaman ya samu tagomashin halartar Shugaban majalissar wakilai ta ƙasa, Femi Gbajabiamila. Ya yin da shi kuwa Kwankwaso ya samu rakiyar zaɓaɓɓen ɗan majalissa, Abdulmumin Jibrin.
Ita kuwa, Mata ga zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar, Sanata Oluremi Tinubu, ta tarbi matar jagora Kwankwaso, Hajiya Salamatu. Inda ganawar ta tuno da tsohuwar alaƙar da ke tsakanin Tinubun da Kwankwaso, tun suna matsayin ƴan majalissa, a shekarar 1992.
Da ya ke martani kan ganawar, mai taimakawa Shugaban ƙasa kan kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad, ya ce ”Za mu yi farin ciki da hakan, tunda dama jam’iyyar mu ta APC a Kano tana bukatar tsayayyen jagoran da zai hada kan ‘yan jam’iyya baki daya”.
Ya yin da wasu daga cikin magoya baya kuwa, ke cigaba da bayyana rashin amincewar su da batun haɗewar, bayan da jagora Kwankwaso ya buƙaci a bashi lokaci, domin tattaunawa da magoya baya.