Za Mu Toshe Dukkannin Hanyoyin Tattalin Arziƙi, Muddin Aka Taɓa Masu Zanga-Zangar Ƙasa – NLC
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan taɓa membobin ƙungiyar, a ya yin zanga-zangar kwanaki biyun da za su gudanar, a faɗin ƙasar nan.
Ta cikin wani jawabi da ƙungiyar ta fitar, a ranar Lahadi, shugaban ya ce, NLC za ta toshe dukkannin wata hanya ta tattalin arziƙi, muddin aka farmaki ko da guda ne, a cikin membobinta da za su gudanar da zanga-zangar.
NLC dai, ta shirya gudanar da zanga-zangar ta kwanaki 2 ne, a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairun da mu ke bankwana da shi, domin nuna fushinta kan halin matsin da tattalin arziƙin ƙasar nan ya tsinci kansa.
Sai dai, tuni hukumar tsaro ta SSS, da Atoni Janar Na Ma’aikatar Shari’a Ta Tarayya, Lateef Fagbemi, su ka roƙi ƙungiyar da ta janye shirinta na gudanar da wannan zanga-zanga, a wani mataki na ƙauracewa doka da oda.
Ta cikin wata wasiƙa da aka aikewa tawagar Lauyoyin ƙungiyar ta NLC, an yi musu tuni kan umarnin Kotun da ya dakatar da su daga gudanar da zanga-zanga.
A nasa martanin, Shugaban na NLC, ya ce ko kaɗan zanga-zangar da za su gudanar ba ta da alaƙa da umarnin da Kotun ta bayar, na dakatar da su daga zanga-zanga.