Labarai

Za Mu Tsige Duk Shugaban Da Ya Yi Fashin Zuwa Ofishinsa – Saƙon Zulum Ga Sababbin Ciyamomi

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya umarci sababbin shuwagabannin ƙananan hukumomin jihar, da su dinga sanya hannu sau huɗu kowacce rana, a rijistar zuwansu ofishi, dan tabbatar da su na zuwa aiki.

Zulum, ya bada wannan umarni ne, ranar Litinin, a birnin Maiduguri, ya yin da ya ke jagorantar bikin rantsar da sababbin shuwagabannin ƙananan hukumomin jihar guda 27.

Zulum, ya kuma umarci Ma’aikatar ƙananan hukumomin jihar, da ta samar da fasahar na’urar ɗaukar dangwalen yatsu a dukkannin ofisoshin shuwagabannin ƙananan hukumomin, a kowacce rana, daga ƙarfe 8 na safiya, rana, ƙarfe 2, da kuma ƙarfe 3:30 na yammaci.

Ya kuma ce, ɗaukar matakin abu ne da ya zama wajibi, domin tantance shuwagabannin da basa halartar ofisoshinsu, ya na mai cewar, dukkannin shugaban da aka samu da laifin rashin halartar ofishinsa, ba tare da wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba, toh! babu shakka hukuncinsa shi ne “tsigewa”.

“Mun shawarci Ciyamomi, lokuta da dama, sai dai mun fuskanci shawarar bata shiga kunnuwansu.

“Yanzu mun ɗauki matakan da zamu tabbatar da zuwan kowannensu Ofishi, wanda hakan ba ƙaramin muhimmanci ya ke da shi ba”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button