Zamu Haɗe Da MTN A Gaban Mai Shari’ah – Alhaji Sani
Fitaccen Ɗan Jaridar nan, wanda ke fafutukar kare martaba da muhibbar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya bayyana cewar, tuni ya umarci Lauyansa da ya aikewa kamfanin sadarwa na MTN Nigeria buƙatar biyansa diyyar Naira miliyan 50, sakamakon tarin asarar da kamfanin ya jawo masa, bayan ɗaukewar igiyar sadarwarsu (Network) a ranar Larabar da ta gabata.
Zanginan ya kuma yi barazanar maka kamfanin a gaban Shari’ah, muddin ya gaza rage masa raɗaɗin asarar da ya fuskanta, ta hanyar biyansa kuɗaɗen tarar.
Idan za a iya tunawa dai, an samu ɗaukewar Network ɗin kamfanin sadarwar na MTN na tsawon sa’o’i, a ranar Larabar da ta gabata, wanda hakan ya jawowa masu amfani da layukan tsayawar al’amuransu, kama daga kan kira, zuwa browsing a shafukan Intanet.
Tun a ranar kuma, MTN ɗin ya fito ya bada haƙuri ga masu amfani da layin nasa, tare da alƙawarin shawo kan matsalar cikin ƙanƙanin lokaci.