Nishaɗi

Zan Mayarwa Da Gwamnan Kano Jikokinsa, Tunda An Dakatar Da Ni Daga Sana’ar Fim – Abdul Saheer

Fitaccen Jarumi a Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Abdul Saheer, wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shirin tashar Arewa24 mai dogon zango na Kwana Casa’in, ya bayyana cewar, zai mayar da ƴaƴan da ya haifa ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tunda an dakatar da shi, daga sana’ar da ya ke amfani da ita wajen iya ɗaukar nauyinsu (Film).

Jarumin, ya bayyana haka ne, ta cikin wani faifan bidiyo da ya fitar, a ranar Talata, inda ya ce, a halin da ake ciki, ba zai iya riƙe ƴaƴayen nasa ba, sakamakon halin rashin sana’ar da ya tsinci kansa a ciki, inda ya riƙo hannayen yaran, tare da shigar da su cikin bidiyon wanda ya fitar.

Abdul Saheer, ya zargi hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, da dakatar da shi ta hanyar rashin adalci, ba tare da jin ta bakinsa ba.

Idan ba a manta ba dai, da yammacin jiya (Litinin) ne, babban Sakataren hukumar ta tace fina-finai, Abba El-Mustapha, ya sanar da dakatar da jarumin daga sana’ar Film har tsawon shekaru biyu, bisa zarginsa da wallafa wani bidiyon batsa, a shafinsa na kafar sadarwar TikTok, lamarin da Jarumin ya musanta.

Jarumi Abdul Saheer, ya bayyana cewar, bidiyon da ya wallafa a shafin nasa, ya na faɗakar da Jama’a ne game da illar shigar banza ko rayuwar lalata, kuma rashin lafiya ce ta tilasta masa gaza halartar gayyatar da hukumar tace fina-finan ta yi masa, domin kare kansa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button