Zan Yi Binciken Ƙwa-Ƙwaf Akan Ma’aikatan Da Ganduje Ya Ɗauka a Gaɓar Ƙarshe – Abba Gida-Gida
A saƙonsa na bikin ranar ma’aikata, zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin sa ke duba game da al’amarin ɗaukar ma’aikata, da Gwamnati mai barin gado ta Abdullahi Umar Ganduje, ke cigaba da gudanarwa, a halin yanzu.
Abba, ya bayyana hakan ne, ta cikin wani saƙo da Babban Sakataren yaɗa labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, a ranar Litinin.
A cewar Gwamnan dai, Gwamnatin mai barin gado, ta aikata almundahana a fagen na ɗaukar ma’aikata, ya na mai jaddada cewar, da zarar an rantsar da gwamnatinsa a ranar 29 ga watan Mayun da mu ke ciki, zai mayar da hankali wajen binciken taɓargazar da ke cikin lamarin.
Ya kuma ce, Gwamnatinsa za ta tabbatar da cewar, waɗanda su ka cancanta, tare da bin hanyoyin da su ka dace, da ma mallakar takardun da ake buƙata ne, su ka rabauta da Aikin.
Abba Gida-Gida, ya kuma ƙara da taya ɗaukacin ma’aikatan Gwamnati, da ma na masana’antu masu zaman kansu da ke jihar, murnar bikin ranar Ma’aikatan ta shekarar 2023.
Kafin ajiye aikinsa dai, Zaɓaɓɓen Gwamnan ya yi Aikin Gwamnati na sama da shekaru 20, a matakai da dama, na ma’aikatar ruwan jihar Kano.
Ka zalika, ya ce ma’aikata su ne ƙashin bayan gudanar da kowacce sahihiyar Gwamnati da ta cimma nasara, wacce kuma ta ɓullo ta hanyar Demokraɗiyya, don haka akwai buƙatar yin sadaukarwa dominsu, da ma karramasu.
Bugu da ƙari, zaɓaɓɓen Gwamnan, ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen farfaɗo da sha’anin aikin Gwamnati, a matsayin wani mataki na ƙarfafa tsarin, dan samun biyan buƙata, ta fuskar Aikin Gwamnati.