Zamantakewa
Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Birnin Kano, Bayan Fitar Kwafin Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara
Wata zanga-zanga mai zafi, ta ɓarke a birnin Kano, bayan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta fitar da kwafin hukuncin da ta yanke kan shari’ar zaɓen Gwamnan Kano.
Zanga-zangar dai, na gudana ne, yanzu haka a yankin gidan Gwamnati zuwa Ɗan-Agundi, ana kuma kyautata zaton membobin jam’iyyar NNPP ne mai mulki ne ke gudanar da ita, bisa zargin rashin samun Adalci daga Kotun ta ɗaukaka ƙara.
Zanga-zangar kuma, ta zo ne, duk da irin gargaɗin da rundunar ƴan sandan jihar ta yi na ƙauracewa yin zanga-zanga, da ma yarjejeniyar zaman lafiya, da jam’iyyun guda biyu na NNPP da APC su ka sanyawa hannu.